• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ABUJA-KADUNA-HAR YANZU BA A SAN INDA FASINJOJIN JIRGIN KASAN DA A KA KAI WA HARI FIYE DA 100 SU KE BA

Mako daya bayan hari kan jirgin kasan fasinja a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, ba a ji duriyar fiye da fasinjoji 100.

Hukumar jiragen kasa ta Najeriya ta ba da karin haske kan yawan fasinjojin da ke cikin jirgin a lokacin da akasin ya faru su 362.

Kazalika an tabbatar da cewa 8 daga fasinjojin sun riga mu gidan gaskiya yayin da wasu da dama su ka samu raunuka.

Wannan shi ne karo na farko da kai tsaye barayin daji su ka kai hari kan jirgin kasan da amfani da nakiyoyi inda su ka bi baya da harbe-harbe.

Babban manajan hukumar jiragen Fidet Okhiria ya ce layin wayar fasinja 51 da a ka rubuta a takardar bayanai bas a shiga yayin da layuka 35 ke shiga amma ba a daukar kiran.

A halin yanzu akwai fasinjoji 186 da su ka tsira har ma su ka isa gidajen su.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “ABUJA-KADUNA-HAR YANZU BA A SAN INDA FASINJOJIN JIRGIN KASAN DA A KA KAI WA HARI FIYE DA 100 SU KE BA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.