• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ABUJA-FILATO-KAR MUTANE SU DAMU DA BARAZANAR TA’ADDANCI-BABBAN SUFETO

Babban sufeton ‘yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba ya ce kar al’ummar Abuja da Filato su damu don barazanar harin ta’addanci da a ka samu.

Wannan na zuwa ne biyo bayan bayanin sirri na ta’addanci da kwamishinonin ‘yan sanda na Abuja da Filato su ka samu.

Usman Alkali ya ce an dau matakan tsaro don kawar da duk wani yunkurin ta’addanci don haka kar mutane su firgita.

Ba mamaki wannan gargadi na da nasaba da yanda ‘yan Boko Haram su ka shiga wasu sassan jihar Neja.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.