• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ABU DHABI TA KARBI WADANDA SU KA SAMU RAUNUKA A AKKAR DON YI MU SU MAGANI

Abu Dhabi ta karbi wadanda su ka samu kunar wuta a yankin Akkar na talakawa a Lebanon don yi mu su magani.

Wannan na daga tsarin aiyukan jinkai don tallafawa Lebanon kula da majinyatan, alhali ta na cikin kalubalen tattalin arziki.

Za a raba majinyatan a ingantattun asibitoci na Abu Dhabi da ke Daular Larabawa.

Akasin na Akkar ya faru ne daga wata tankan mai da a ka kwace, sai cikin mamaki gobara ta kama har fiye da mutum 30 su ka mutu, 79 su ka samu raunuka.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.