• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ABOKAN TAKARA KU BA NI GOYON BAYA -SABON SHUGABAN APC ABDULLAHI ADAMU

Sabon shugaban jam’iyyar APC mai mulki a taraiya, Abdullahi Adamu ya bukaci sauran abokan takarar sa a neman shugabancin su hadu su ba shi goyon baya.
Sanata Adamu wanda ya zama shugaban APC a babban taron jam’iyyar ba tare da kada kuri’a, ya ce shi dama ba ya shakkar kada kuri’ar don Allah ya taimake shi bai taba takara ya sha kaye ba.
Sabon shugaban na cewa ya na da kyau sauran abokan takarar su dauka a duk takara mutum daya ne zai lashe don haka akwai bukatar rungumar kaddara.
Game da tsufa ko yawan shekaru da a ke ganin za su hana Adamu aiki cikin kuzari, Sanata Adamu ya ce aikin da kwarewa a ke yi ba karfin gangar jiki ba.
Hakanan Adamu ya nuna ba ya ganin an taka doka ko an yi abun da ya saba ka’ida ya kyale ba, duk da ya na aikin ko hukunci cikin hikima.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “ABOKAN TAKARA KU BA NI GOYON BAYA -SABON SHUGABAN APC ABDULLAHI ADAMU”

Leave a Reply

Your email address will not be published.