• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ABIN MAMAKI A BICHI WAJEN DAURIN AUREN YUSUF BUHARI

Manyan ‘yan siyasa sun yi dafifi a masarautar Bichi don shaida daura auren dan sa Yusuf da Zahra.

Amaryar ‘yar Sarkin Bichi ce Nasiru Ado Bayero.

Abun da ya fi daukar hankali shi ne zuwan tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar wanda ya gaisa da shugaba ba tare da bangarorin biyu ba sun duba bambancin siyasar APC da PDP ba ko takarar shugabanci da us ka fafata har kotun koli a zaben 2019.

Kazalika tsohon shugaba Jonathan ma ya zo bukin, amma zuwan sa bai dau hankali ba fob yanda a ka ganin sa ya na ziyara da dariya a fadar Aso Rock.

Gwamnoni ma da dama sun halarci daura auren da ministan sadarwa Isa Pantami ya jagoranta, wanda shi ne ya kan shiga gaba a lamuran musulunci na fadar gwamnatin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
59 thoughts on “ABIN MAMAKI A BICHI WAJEN DAURIN AUREN YUSUF BUHARI”

Leave a Reply

Your email address will not be published.