Sabon shugaban jam’iyyar APC mai mulki a taraiyar Najeriya a yanzu Abdullahi Adamu ya ajiye kujerar sa ta majalisar dattawa daga mazabar Nassarawa ta yamma.
A wasika ga shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan, sabon shugaban na APC ya ce biyo bayan zabar sa a matsayin shugaban APC a babban taron jam’iyyar ya sa shi daukar matakin na murabus.
Adamu ya godewa shugaban dattawan bisa yanayin shugabancin sa duk da cewa duk ‘yan jam’iyyar APC ne kuma sun yi aiki tare wajen yaki da tsohon shugaban majalisar dattawan Bukola Saraki.
Kazalika shi ma sabon mataimakin shugaban APC na arewacin Sanata Abubakar Kyari ya yi murabus daga majalisar dattawa.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
I was pretty pleased to discover this great site. I need to to thank you for your time for this particularly fantastic read!! I definitely appreciated every part of it and I have you book marked to see new stuff on your blog