• Mon. May 23rd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ABDULKARIM DAUDA MUKE SO YA ZAMA GWAMNAN JAHAR KATSINA A ZABEN 2023-AHIJO

A yayin da aka shiga shekarar jajiberar siyasa a Nijeriya akan babban zaben da za’ayi a shekarar 2023, ko wace jaha masoya na nuna goyon bayan wanda suke ganin ya cancanci ya fito takara don lashe zaben na badi.

A jahar Katsina ma, masoya sunata kira ga Alhaji Abdulkarim Dauda Daura daya fito ya tsaya takarar gwamnan jahar Katsina a babban zaben badi don ganin cancantar shi.

Ahmed Ahijo Wali matashin dan siyasa ne a jahar Katsina, mun tattauna dashi inda ya bayyana ra’ayinsa cewa “Abdulkarim Dauda mutum ne mai asali, Mahaifinsa Malam Dauda Daura (Durbin Daura), shine ya yayi chairman na kungiyar NAGGE DADI GOMA data nemo jahar Katsina watau KATSINA STATE, wannan ya tabbatar mana yana da wani asali na kishin Jahar Katsina tun daga baya har zuwa yanzu”.

Ahijo ya kara da cewa “Kuma idan muka kalli halin da muke ciki a ayau, muna bukatar mutum irin Alhaji Abdulkarim Dauda ne, saboda mutum ne mai tsoron Allah, kamar yadda abokansa suke shaida mana hakan, tun suna kanana hakan yake, kazalika yayin da yake aikin gwamnati ma, sannan kuma mutum ne mai tausayi don yanzu a halin da muke ciki muna bukatar mutum mai tausayi ne, na san irin yadda yake taimakwa mutanen da suka shiga mawuya cin hali na rayuwa a kowane bangare, da kuma taimakawa wajen samarwa da matasa aikin yi”.

Wannan shine kiran da matasa ke yiwa Alhaji Abdulkarim Dauda Daura don ya fito takarar gwamnan jahar Katsina a babban zaben shekara 2023, da fatan Abdulkarim Dauda zai ji kiran da sukeyi masa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
48 thoughts on “ABDULKARIM DAUDA MUKE SO YA ZAMA GWAMNAN JAHAR KATSINA A ZABEN 2023-AHIJO”

Leave a Reply

Your email address will not be published.