• Wed. Dec 1st, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ABDULJABBAR YA BA DA HAKURIN KALAMAN SA NA BATANCI GA JANIBIN MANZON ALLAH

Abduljabbar Kabara wanda ya halarci zaman mukabala da malamai a Kano kan tubumar batanci ga manzon Allah ya fitar da faifai na neman ahuwar munanan kalaman da ya yi amfani da su.

Malamin wanda a ka dakatar don irin yanda ya ke karyata hadisan da ke Sahihul Bukhari, ya ce matukar abun da ya ke fada ya sabawa abubuwan da ya ke ikirari, to ba sai an je lahira ba ya tuba.

Wannan neman ahuwa ta zo ne kwana daya bayan mukabalar da a ka gudanar inda malamun ya kasa nuna hadisan da ya ce na karya ne ko kuma wadanda ya ke amfanu da su wajen samun damar furta kalamai masu muni ga manzon Allah da sahabban sa.

Yanzu dai za a gabatar da rahoton sakamakon mukabalar a rubuce ga gwamnatin Kano don daukar matakin da ya dace.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *