• Tue. Nov 30th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ABDULJABBAR BAI KAWO HUJJOJI BA A MUKABALA-SALISU SHEHU

Alkalin mukabala tsakanin Abduljabbar Nasiru Kabara da malamai a kano Sheikh Salisu Shehu ya ce malamin bai kawo hujjojin kare kan sa ba a mukabalar.

Bayan kammala mukabalar, Sheikh Shehu ya ce Abduljabbar bai kare kan sa ba don haka bai samu galaba a mukabalar ba.

Malamai sun kawo bayanan yanda Abduljabbar ya yi ta cin zarafin sahabbai da hakan ya kai kan manzon Allah mai tsira da aminci.

Tun farko Abduljabbar ya zo da littattafai cikin mota don mukabalar amma bai bude ko daya daga ciki ta ba da wata hujja ba.

Kwamishinan lamuran addini na jihar Kano Muhammad Tahar wanda ya gamsu cewa Abduljabbar bai amsa tambaya ba, ya ce zai mika rahoton ga gwamna Abdullahi Umar Ganduje don daukar mataki a gwamnatance.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *