• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ABBA KYARI BA SHI DA LAIFI HAR SAI KOTU TA TABBATAR-BARISTA HAMZA DANTANI

Lauya mai magana a madadin DCP Abba Kyari ya ce har yanzu ba za a iya dora laifi ga Kyari ba sai kwamitin bincike na shari’a ko kotu sun yanke hukunci.
Lauyan Barista Hamza Dantani ya ce hatta faifan bidiyo da a ka nuna Kyari a mota da wani kamar a na rashin gaskiya kan kwaya, ba lalle batun kwaya ba ne, don Kyari kan kama masu fataucin kwaya da neman sajewa da masu sayar da kwaya don hikimar damke miyagun iri.
Dantani ya ce Kyari mutum ne don haka zai iya kuskure a yayin gudanar da aiki, amma in an duba aiyukan san a alheri za su rinjayi akasin haka yawa.
Lauyan ya bukaci masu tababar gaskiyar Kyari su jira a kammala dukkan bincike har gaskiya ta yi halin ta, maimakon yanke hukuncin riga malam masallaci.
Bisa dokokin Najeriya duk wanda a ke zargi a wanke ya ke har sai an yanke hukuncin karshe

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.