• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

ABBA GIDA-GIDA YA SAMU TIKITIN TAKARAR NNPP A ZABEN GWAMNAN KANO

Abba Kabir Yusuf wanda a ka fi sani da Abba Gida-Gida ya samu nasarar zama dan takarar jam’iyyar NNPP na zaben gwamnan jihar Kano.

Gida-Gida ya samu nasarar a zaben fidda gwani da a ka gudanar a filin wasa na Sani Abacha a Kano ba tare da hamaiya ba.

Yusuf wanda shi ya yi wa PDP takarar gwamnan Kano a 2019 amma gwamna Ganduje na APC ya yi nasara a kan sa, surukin tsohon gwamnan jihar ne Rabiu Musa Kwankwaso.

NNPP dai na daga jam’iyyu da a ke ganin za su yi tasiri a zaben 2023 musamman a wasu yankunan arewacin Najeriya inda mabiya Kwankwaso ke da yawa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.