• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

A YAU MABIYA ADDININ KIRISTA A FADIN DUNIYA KE BUKIN KIRSIMETI

ByNoblen

Dec 25, 2021 ,

A yau asabar din nan 25 ga watan nan na disamba 2021 mabiya addinin kirista a fadin duniya ke bukin kirsimeti.
Bukin da ke tuna haihuwar Annabi Isa Alaihis Salam shekara 2021, ba dukkan mabiya addinin kirista ke yin sa ba, don akwai wadanda ba su amince da sahihinacin yin bukin ba.
A Abuja babban birnin Najeriya an sa kananan fitilun wuta don ado a manyan tituna da kasuwanni amma a gaskiya wasu gidaje da a baya su kan sa wannan wuta ba su saka ba.
Rashin saka irin wannan wuta ba zai rasa nasaba da koma bayan tattalin arziki ba inda mutane ke zabar kashe kudi kan lamuran da su ka zama wajibi.
Babban sufeton ‘yan sanda Usman Baba ya ba da umurnin ga kwamishinonin ‘yan sanda a jihohi su tabbatar jami’an sun a zuba ido kan lamuran tsaro dare da rana daga ranar kirsimeti zuwa sabuwar shekarar miladiyya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *