• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

A TUHUMI NGOZI OKONJO IWEALA DON YANDA TA KI TSAWATAWA TWITTER – ADAMU GARBA

Matashi mai kamfanin dillancin dabarun aiki da yanar gizo Adamu Garba ya bukaci a tuhumi shugaban hukumar kasuwanci ta duniya Ngozi Okonjo Iweala don yanda ta gaza tsawatawa kamfanin twitter kan ba da damar da ya yi ‘yan awaren Biafra na yada miyagun bayanai da ke barazana ga Najeriya.

A zantawa da a ka yi da shi ta wani shirin talabijin na Channels, Garba ya ce Iweala ta na cikin daraktocin kamfanin twitter amma ta yi shiri ba ta tsawatawa alhali wasu dun dage wajen cinnawa kasar ta, ta haihuwa wuta.

Garba wanda ya yi yunkurin takarar shugabancin kasa a 2019 amma ya ce ya janye don shugaba Buhari, ya taba daukar matakin kai karar twitter gaban kotu don yanda kamfanin ya ba da damar yayata zanga-zangar endsars.

A yanzu haka ma, matashin da kan yi mu’amalar aiki da kamfanin “microsoft” na Bill Gates, na shirin kai karar twitter kotu.

Masu caccakar Garba na nuna ya na daukar matakai ne don neman suna kodaya ke manufofin sa na da ma’ana.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
44 thoughts on “A TUHUMI NGOZI OKONJO IWEALA DON YANDA TA KI TSAWATAWA TWITTER – ADAMU GARBA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.