• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

A TSAKIYAR WATAN GOBE ZA A FARA AIKIN HAJJI NA BANA

ByNoblen

Jun 25, 2021 , ,

Hajjin bana hijra 1442 zai fara daga tsakiyar watan gobe inda hukumomi su ke cikin shiri a babban masallacin haramin Makkah don kula da alhazai.

Kamar yanda a ka baiyana alhazai dubu 60 ne daga iya cikin Saudiyya za su gudanar da aikin hajjin.

Hukumomin sun kara baiyana cewa za a bar masu aikin ne daga shekaru 18 zuwa 65 su yi aikin kuma bayan samun rigakafin korona.

Ba karin bayani kan yanda kasar za ta zabi wadanda za su yi aikin tun da a ranar farko kadai da a ka bude rejista ta yanar gizo an samu fiye da mutum dubu 400 da ke son shiga aikin hajjin.

Bara ma da a ka yayata mutum dubu 10 ne za su yi aikin, karshen an samu mutum dubu daya ne su ka yi aikin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
5,913 thoughts on “A TSAKIYAR WATAN GOBE ZA A FARA AIKIN HAJJI NA BANA”