• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

A TALLAFAWA NAJERIYA WAJEN YAKAR ‘YAN TA’ADDA-SHUGABA BUHARI A TARON TURKIYYA

ByNoblen

Dec 19, 2021 ,

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mika bukata a wajen taron tattalin arzikin Afurka da Turkiyya na 3 da a ka gudanar a kasar Turkiyya da a kawowa Najeriya daukin yaki da ta’addanci.
Shugaban ya nuna farin ciki cewa taron da shugaban Turkiyya Raceb Tayyeb Erdoan ya shirya taron, ya ba da muhimmanci kan batun yaki da ta’addanci.
Mai taimakawa shugaban Najeriya kan labaru Garba Shehu ya ruwaito shugaban na cewa duk da yanda a ka lallasa ‘yan ta’addan Boko Haram, har yanzu su na nan da kaifin su, da kai hari kan fararen hula.
Hakanan shugaban ya buakci daukar matakan tunkarar kalubalen sauyin yanayi da ke addabar Najeriya, Turkiyya da ma sauran sassan duniya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *