• Thu. Dec 9th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

A TAIMAKA A DAWO MA NA DA SHAGUNAN MU A FILIN JIRGIN ABUJA-‘YAN KASUWA

Wasu daga ‘yan kasuwar da su ka rasa shagunan su a tsohon ginin sashen zirga-zurgar jirage na cikin gida a filin daukar jiragen sama na Abuja Nnamdi Azikwe sun koka kan rasa shagunan su.

Wannan ya faru ne bayan kaurowa sabon gini inda kuma a ka gina sabon ginin kula da fasinjojin ketare.

Alhaji Adamu na daga cikin ‘yan kasuwar da ke rakube daya don jiran tsammanin samun shaguna a sabon ginin.

Adamu ya ce shi da sauran abokan sa ‘yan kasuwa sun fara huldar su a filin jirgin tun 1988 zamanin mulkin Janar Ibrahim Babangida.

Adamu ya ce wasu mutane sabbi su ka amfana da shaguna zuwa yanzu kuma akwai sauran gurabe masu yawa da za su so ministan jiragen sama Hadi Sirika ya ba su don gudanar da harkokin su kamar yanda su ka shafe shekaru da dama su na yi.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *