• Tue. Oct 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

A SANAR DA MU TA KOWANE FILIN JIRGI A KA GA OBIANO ZAI FICE DAGA NAJERIYA-EFCC

ByYusuf Yau

Nov 26, 2021

Hukumar yaki da cin hanci ta Najeriya EFCC ta bukaci hukumar shige da fice ta sanar da ita a duk lokacin da a ka ga gwamnan Anambra Willie Obiano na shirin ficewa daga Najeriya.
Jaridar THE WILL ta baiyana cewa da alamu akwai labarin sirri da a ka samu na shirin arcewar gwamnan bayan kammala wa’adin mulkin sa.
Willie Obiano dai zai kammala wa’adin sa a ranar 16 ga watan Maris na 2022 inda zai mika mulki a hukumance ga Charles Chukwuma Soludo da ya lashe zaben gwamnan jihar na 10 ga watan nan.
Wannan ya nuna EFCC ta sanya Obiano a jerin mutanen da ta ke saka ido a kan su don cafke su in sun yi shirin arcewa.
Jami’in labarun hukumar Wilson Uwujeren ya ce ba a tuntube shi kan batun ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “A SANAR DA MU TA KOWANE FILIN JIRGI A KA GA OBIANO ZAI FICE DAGA NAJERIYA-EFCC”

Leave a Reply

Your email address will not be published.