• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

A NINKA TAIMAKO YAYIN DA AZUMIN RAMADAN YA SHIGO-MALAMAI DA MASU SHARHI

ByNoblen

Apr 13, 2021

A yayin da azumin watan ramadan na bana ya shigo, malamai da sauran masu sharhi na bukatar ninka taimako don tallafawa talakawa da sauran masu karamin karfi.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da farashin kayan masarufi ya yi tashi da akalla kashi 50%.

Tuni masallatai su ka fara tanadin abubuwan da za su rika taimakawa miskinai a wajen shan ruwa ta hanyar tara taimako daga wajen jama’a. Hakanan wasu masallatan ma sun yi sabon fenti da inganta fomfuan alwala ko samarda sabbin butoci.

Nan Alaramma Alhaji Usman Ladan ne da ke kasuwanci a Abuja ke baiyana yands lamuran kasa su ke a watan da a ke bukatar kyautatawa.

Daya daga manyan limaman babban masallacin Abuja Dr.Muhammad Kabir Adam ya ce a na samun lada mai yawa a watan mai albarka.

Shehun malamin Islama Imam Abdullahi Bala Lau ya ambaci muhimmancin tallafawa marayu a wannan lokaci.

Yayin da a ke bude tafsirai cikin saukin matakan kariya daga cutar korona bairos, masu neman taimako kan yi amfani da damar wajen dagewa su tara abinda za su ci har zuwa ranar sallah.

Koma dai me za a ce, akwai duk kayan da a ke bukata a kasuwa kama daga shinkafa, dankalin turawa zuwa tattasai da tumatur, amma farashin ne ya fi karfin aljihun masu karamin karfi da su ne mafiya rinjaye da samun su bai fi dala daya a wuni ba da ya ke zama mizanin talauci na duniya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “A NINKA TAIMAKO YAYIN DA AZUMIN RAMADAN YA SHIGO-MALAMAI DA MASU SHARHI”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *