• Mon. May 23rd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

A NA ZARGIN RASHA NA AIKATA LAIFUKAN YAKI A MAMAYAR UKRAINE

A na zargin dakarun kasar Rasha da aikata laifukan yaki a mamayar da kasar ke yi wa Ukraine ta hanyar hallaka fararen hula.

Kungiyar kare hakkokin ‘yan-adam ta HUMAN RIGHTS WATCH ta baiyana cewa dakarun Rasha na aikata laifuka a sassan da su ke da karfi kamar Chernihiv, Kharkiv da Kyiv.

Wannan zargi ya zo ne bayan samun gawawwakin mutane a zube a kan titunan garin Bucha da ke kusa da Kyiv, kwana uku bayan Rasha ta janye daga yankin.

Ministan tsaron Rasha ya musanta kashe mutane a Bucha ya na mai cewa tun ranar 30 ga watan jiya dakarun su, su ka janye don haka hotunan da a ka nuna na neman tada fitina ne.

Rasha ta baiyana cewa ta na kai hari ne don kwance damarar yakin Ukraine, don haka kan cibiyoyin soja kawai ta ke daukar mataki ba kan farar hula ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
10 thoughts on “A NA ZARGIN RASHA NA AIKATA LAIFUKAN YAKI A MAMAYAR UKRAINE”
  1. I cling on to listening to the news broadcast speak about receiving free online grant applications so I have been looking around for the finest site to get one. Could you advise me please, where could i acquire some?

  2. Good ?V I should certainly pronounce, impressed with your site. I had no trouble navigating through all tabs and related information ended up being truly easy to do to access. I recently found what I hoped for before you know it at all. Quite unusual. Is likely to appreciate it for those who add forums or anything, site theme . a tones way for your customer to communicate. Nice task..

Leave a Reply

Your email address will not be published.