Mutane na baiyana wasu lamura na dabi’un kirki na wasu daga ‘yan tawagar marigayi babban hafsan sojan kasan Najeriya Ibrahim Attahir.
Manjo Hayat na cikin ‘yan tawagar da a ka ba da labarin ya na azumin sitta shawwal har ma ya bugawa mahaifiyar sa zai zo shan ruwa inda daidai 6 na yamma hatsarin ya auku.
Hakanan shi ma Burgediya Janar Kuliya an yada wani sakon addu’a da ya tura ta manhajar WhatsApp da ke nuna fatan gamawa da duniya lafiya da sauki yayin da a ka tsinci kai a kabari. An gudanar da sallar jana’iza ta “GA’IB” ga marigayin a Kano don nuna juyayi ga rashin sa.
Hatta shi kan sa Janar Attahiru an nuna sai da ya halarci sallar jumma’a a Abuja kafin tafiya filin jirgi inda ya shiga tafiyar da ta zama sanadiyyar ajalin sa.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀