• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

A NA TA BINCIKEN SAHIHANCIN LABARIN MUTUWAR SHUGABAN BOKO HARAM SHEKAU

Labaru sai karuwa su ke yi a wasu kafofi cewa shugaban ‘yan Boko Haram Abubakar Shekau ya mutu a dajin Sambisa.

Abun da a ka baiyana shi ne ‘yan ta’addan ISWAP ko DAESH na Afurka ta yamma su ka kutsa dajin har su ka tarar da Shekau inda ya yi saranda da amincewa da sauya wasu manufofin sa na salon ta’addanci.

A cikin wannan yanayi ya tada makami duk su ka sheka lahira.

Hatta rundunar sojan Najeriya na nuna ta na kan binciken sahihancin labarin ne.

A baya an sha samun labarin Shekau ya mutu amma sai ya baiyana a faifan bidiyo ko sauti ya na cewa ya na nan kuma zai cigaba da muradun sa.

Koma dai me za a ce, ya na da kyau a kara jiran sahihin binciken gaskiyar lamarin.

BABBAN BASARAKE A GOMBE YA RIGA MU GIDAN GASKIYA

Babban basaraken masarautar Funakaye a jihar Gombe Muhammad Abubakar Kwauranga ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayin dai zuriyar ginshikin masarautar Gombe ne wato Modibbo Babayero wanda ya karbo tuta daga Shehu Usman Danfodio.

Marigayin ya hau sarauta a 2010 bayan rasuwar mahaifin sa Abubakar Kwairanga wanda ya nemi sarautar Gombe a shekarun 1980 amma kanin sa marigayi Shehu Usman Abubakar ya yi nasara a kan sa.

Gwamnan Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya na daga wadanda su ka halarci jana’izar marigayin a garin Bajoga da ke arewacin Gombe daf da kamfanin siminti na Ashaka.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
42 thoughts on “A NA TA BINCIKEN SAHIHANCIN LABARIN MUTUWAR SHUGABAN BOKO HARAM SHEKAU”
  1. Hi there, just became alert to your blog through Google, and found that it is truly informative. I’m gonna watch out for brussels. I’ll be grateful if you continue this in future. Many people will be benefited from your writing. Cheers!

Leave a Reply

Your email address will not be published.