A na sa ran gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni zai dawo Najeriya daga Daular Larabawa, inda hakan zai taimaka wajen gane tahakikanin dambarwar shugabanci da a ke yi a jam’iyyar.
Mala Buni wanda ya fita waje don ganin likita kan jinyar da ba a baiyana ba, ya bar baya da kurar batun ya na kan mukamin sa ne ko an sauya shi da gwamnan Neja Abubakar Sani Bello.
A yanzu haka dai gwamna nna Neja ke gudanar da lamuran jam’iyyar inda a ke ganin ‘yar takaddamar ka iya sanya sake dage babban taron jam’iyyar, ko kuma a gudanar da shi ba kamar yanda a ka yi tsammanin girman taron ba.
Masana siyasa na cewa ta kan yiwu a zo a gabatar da sunan mutum daya a ce an amince ya zama sabon jam’iyyar ba hamaiya daga nan sassa su gabatar da sauran membobin kwamitin gudanarwa.
A gaskiyar magana, gwamnoni na da tasiri ainun kan lamuran jam’iyyu biyu da su ka yi mulkin Najeriya a sabuwar dimokradiyya da ta faro daga 1999.
Helkwatar jam’iyyar dai na cigaba da musanta samun wani canjin shugabanci.
A NA SA RAN DAWOWAR GWAMNA MAI MALA BUNI A LARABAR NAN DON WARWARE TAKADDAMAR APC

KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
I got this website from my pal who told me regarding
this web site and at the moment this time I am visiting this site and reading very informative
posts here.
Thanks for one’s marvelous posting! I certainly
enjoyed reading it, you’re a great author.I will ensure that I bookmark your blog and will eventually come back
from now on. I want to encourage that you continue your great work, have a nice
morning!