• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

A NA GWABZA FADA A ZAGAYEN BABBAN BIRNIN UKRAINE, KYIV INDA FICEWAR MUTANE KE SAMUN TANGARDA

ByNoblen

Mar 13, 2022

A na gwabza fada a zagayen babban birnin kasar Ukraine wato Kyiv da hakan ya sanya ficewar farar hula lami lafiya ke zama cikin tangarda.
Rasha na kara zafafa hare-hare don kwance damarar yakin Ukraine da kuma yin takatsantsan don kar hakan ya rutsa da farar hula.
Gwamnatin Ukraine na kokarin amfani da tsarin tsagaita wuta don ficewar farar hula da amfani da irin wannan tsari da a ka yi a birnin Mariupol na kudancin kasar.
Rasha na cigaba da yi wa garuruwan Ukraine kofar rago don kammala wannan muradi na kawar da gwamnatin shugaba Volodymyr Zelenskyy da ke da mubaya’a ga yammacin turai.
Amurka da kasashen yamma na kara nauyin takunkumi kan Rasha don matsa ma ta lamba ta sassauta matakan da ta ke dauka.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “A NA GWABZA FADA A ZAGAYEN BABBAN BIRNIN UKRAINE, KYIV INDA FICEWAR MUTANE KE SAMUN TANGARDA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.