• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

A NA GAB DA GANO RIGAKAFIN ZAZZABIN CIZON SAURO

Wani abun farin ciki na nuna a na gab da gano rigakafin zazzabin cizon sauro da ke addabar kasashen Afurka musamman na yankin sahara.

Yanzu haka an kai kusan kashi 75% na nasarar gwajin rigakafin ta hanyar gudanar da gwaji kam yara a Burkina Faso.

An dade a na nazartar hanyar da za a maganace zazzabin cizon sauro tun 1910 don yanda a ka fahimci zazzabin na kashe dubban mutane duk shekara.

Wannan babban nasarar ce ga hukumar lafiya ta duniya in a ka kammala tabbatar da ingancin rigakafin.

A duk shekara mutum 400,000 ke mutuwa a sanadiyyar kamuwa da zazzabin cizon sauro a duniya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *