• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

A NA CIGABA DA ZUWA TA’AZIYYA GIDAN JANAR ATTAHIRU

Mutane daga sassan Najeriya masu fada a ji na zuwa gidan babban hafsan rundunar sojan kasa Laftanar Janar Ibrahim Attahiru wanda ya rasu da abokan aikin sa sanadiyyar hatsarin jirgin sama.

Kama da wasu gwamnoni zuwa dattawa da malaman addini na zuwa gidan marigayin don jajantawa.

Shugaban JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau na daga manyan malaman da su ka je gidan marigayin don isar da ta’aziyya da addu’ar rahama ga marigayan.

Tsohon darakta a gwamnatin taraiya kuma babban daraktan JIBWIS Ahmad Ibrahim Lau na cikin tawagar.

Ta’aziyya da tausayawa iyalin marigaya na da lada mai yawan gaske.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.