• Thu. May 19th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

A NA CIGABA DA NUNA JUYAYIN HARI KAN JIRGIN KASA DAGA ABUJA ZUWA KADUNA

Jama’a na cigaba da jajantawa kan harin da barayin daji su ka kai kan jirgin kasan fasinja da ya taso daga Abuja don kai jama’a tashar Rigasa da ke Kaduna.
In za a na bin labaru, harin ya yi sanadiyyar asarar ran fasinjoji, samun raunuka da figicin gaske, hakanan da jefa tsoro don ba a yi aunen miyagun irin za su iya kai irin wannan gagarumin harin ba.
Wadanda su ka samu raunuka na karbar magani a asibitin sojoji da ke Kaduna inda a ke cigaba da mika ta’aziyya ga ‘yan uwan wadanda su ka rasa ran su.
Shugaba Muhammadu Buhari ya ba da umurnin a tabbatar da ceto wadanda miyagun irin su ka sace da kara dagewa wajen maganin ‘yan bindigar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “A NA CIGABA DA NUNA JUYAYIN HARI KAN JIRGIN KASA DAGA ABUJA ZUWA KADUNA”
  1. I’m not sure where you’re getting your info, but great topic. I must spend some time learning more or working out more. Thank you for excellent information I was looking for this information for my mission.

Leave a Reply

Your email address will not be published.