• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

A NA CIGABA DA KAMFEN DIN NEMAN LASHE ZABEN EDO MUSAMMAN TSAKANIN APC MAI MULKI A TARAIYA DA PDP MAI MULKI A EDO

Kamfen na kara armashi na zaben gwamnan Edo da hukumar zaben Najeriya za ta gudanar a ranar asabar din nan mai zuwa 19 ga watan nan na satumba. Manyan jam’iyyu biyu APC da PDP ke musayar hamaiyar siyasa a tsakanin su don jawo hankalin jama’a su mara mu su baya. Gwamnan jihar Godwin Obaseki ya nuna rashin jin dadin yanda uban jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya bukaci al’ummar jihar kar su zabe shi, su zabi Pastor Ize Iyamu na APC. Obaseki na nuna tamkar Tinubu ba dan jihar Edo ba ne don haka bai dace ya sanya baki a lamuran zaben jihar ba. Korafin Obaseki ba zai yi amfani a siyasance ba don kowane dan jam’iyyar na yin kamfen ne don nasarar jam’iyyar a dukkan matakai. Akwai alamun tsaurara tsaro don gudun tada fitina a zaben inda rundunar ‘yan sanda ta tura manyan jami’ai don kula da tsaro a zaben da haramtawa ‘yan sanda da ke raka manya ‘yan siyasa fitowa a ranar zaben.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “A NA CIGABA DA KAMFEN DIN NEMAN LASHE ZABEN EDO MUSAMMAN TSAKANIN APC MAI MULKI A TARAIYA DA PDP MAI MULKI A EDO”
  1. always i used to read smaller articles which as well clear their
    motive, and that is also happening with this article which I
    am reading at this time.

Leave a Reply

Your email address will not be published.