‘Yan uwa da sauran jama’a na isar da ta’aziyyar mutuwar tsohon babban hafsan sojan kasan Najeriya Janar Muhammad Inuwa Wushishi.
Marigayin wanda ya zama shugaban sojojin kasan a zamanin gwamnatin farar hula ta Shehu Shagari a 1981, ya rasu ne a London.
Janar Inuwa Wushishi daga yankin masarautar Kontagora a jihar Neja ya yi ritraya daga soja a matsayin laftanar janar.
Gwamnatin Neja ta baiyana rasuwar da nuna juyayi na rashin babban tsohon hafsan sojojin.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀