• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

A KARA HIMMA WAJEN TALLAFAWA MARAYU DA MISKINAI-SHEIKH BALA LAU

Shugaban JIBWIS Imam Abdullahi Bala Lau ya sake nanata kira na duk masu hannu da shuni da ma dai duk masu dan sukuni su kara dagewa wajen tallafawa marayu da miskinai.

Shehun malamai wanda a yanzu haka ya ke gabatar da tafsirin ramadan a Jimeta jihar Adamawa, ya ce farantawa marayu rai musamman da kayan sallah na da lada mai yawa.

Malamin wanda ya saba jan hankalin mutane wajen amfani da albarkar lokacin ramadan wajen dagewa ga ibada, ya bukaci takarkarewa ga tsayuwar ibada ta dare don neman taimakon Allah ga kawo karshen tabarbarewar tsaro da kuncin tattalin arziki.

A wannan dan tsakanin a ke sa ran samun daren lailatul kadr da a cikin sa ne a ka saukar da Alkur’ani mai girma inda dacewa da ibada a ciki na samar da lada da darajar sa ta fi tsawon ta wata 1000.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “A KARA HIMMA WAJEN TALLAFAWA MARAYU DA MISKINAI-SHEIKH BALA LAU”
  1. What’s Going down i am new to this, I stumbled upon this I’ve
    discovered It positively helpful and it has helped me out loads.

    I am hoping to contribute & aid other customers like its helped me.
    Good job.

Leave a Reply

Your email address will not be published.