• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

A JUMMA’AR NAN SHEKARA TA 2021 MILADIYYA TA KE BANKWANA

A jumma’ar nan shekarata ta 2021 miladiyya ta ke kawo karshe inda ya nuna asabar din nan ta zama daya ga watan shekara ta 2022 miladiyya.
Shekarar ta na dauke da abubuwa da dama da su ka hada da fargabar karin farashin man fetur a Najeriya da hakan bai yiwu ba watakila sai a wannan sabuwar shekara.
Hakanan majalisaar dokokin Najeriya ta amince dokar sashin man fetur da ta samu sanya hannu daga sashen zartarwa; duk da haka dokar zaben ‘yar tinkea fidda ‘yan takara da tura sakamakon zabe ta na’ura ba ta kai labara ba don shugaba Buhari ya ki amincewa da ita.
Wani abu mai daukar hankali shi ne rufe layukan sadarwa da a ka yi a jihohin arewa maso yamma da ke fama da ‘yan bindiga don hakan ya zama hanyar rage karfin barayin mutane. Hakan dai bai yi tasiri na zahiri ba don an cigaba da sacewa da ma kona mutanen da ran su.
A shekarar ce a ka cafke shugaban ‘yan awaren Biyafara Nnamdi Kanu daga kasar Kenya inda a ka dawo da shi Najeriya don fuskantar shari’ar cin amanar kasa da ta’addanci.
An abubuwan juyayi a yankin kudu maso gabar inda ‘yan aware kan kashe ‘yan arewa da ke sana’a a can da ma fille kan su ko babbaka su da wuta. A Owerri jihar Imo ma ‘yan bindigar sun yi kisan gilla ga tsohon mai ba wa shugaba Jonathan shawara kan siyasa Barista Ahmed Ali Gulak.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *