• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

A HUKUNTA DUK WANDA YA BI TA BARAUNIYAR HANYA YA NA AIKI DA TWITTER-MALAMI

Miniatan shari’ar Najeriya Abubakar Malami ya fitar da tanadin doka na hukunta duk wanda ya bi ta barauniyar hanya don lalle ilalla sai ya yi aiki da twitter.

Malami na nufin dirar mikiya kan wadanda su ke bin wata manhajar kamfanoni masu zaman kan su da ke aiki ta hanyar bayan fage “VPN” don hawa shafin twitter.

VPN kan tura mai bukata ya hau twitter ta amfani da wata kasar waje da ba ta haramta twitter sai ya cigaba da tura sakonnin sa.

Da alamun daga fitar da sanarwar wasu hukumomin gwamnati da ke kauce hanya su hau twitter ta VPN sun rufawa kan su asiri.

Masana na cewa hanyar VPN na da hatsari don masu satar bayanai kan iya shiga salular mutum cikin sauki su ga duk abun da mutum ke yi da daukar bayanai musamman na sirri da na banki.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
25 thoughts on “A HUKUNTA DUK WANDA YA BI TA BARAUNIYAR HANYA YA NA AIKI DA TWITTER-MALAMI”

Leave a Reply

Your email address will not be published.