• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

A BA NI NNAMDI KANU ZAN HANA SHI SURUTAI DON IGBO NA GIRMAMA NI-MBAZULIKE AMAECHI

ByNasiru Adamu El-hikaya

Nov 20, 2021

Dattijon kabilar Igbo mai shekaru 93 Chief Mbazulike Amarchi ya jagoranci tawaga zuwa fadar Aso Rock inda ya bukaci shugaba Buhari ya ba shi shugaban ‘yan awaren Biyafara IPOB Nnamdi Kanu ya tafi da shi don zai iya hana shi surutan da ya ke yi.
Amaechi wanda ya na daga cikin ‘yan majalisar dokoki a jamhuriya ta farko, ya ce a na matukar girmamashi a kasar Igbo kuma ba ya son barin baya da kura in ya bar duniya.
Amaechi ya ce yanzu haka kasuwanci da sauran lamura sun rikice a kasar Igbo; ya na mai bukatar shugaba Buhari ya zama wanda za a tuna shi a matsayin mai kashe wutar fitina in ta kama.
Shugaba Buhari ya ce wannan lamari ya na hannun kotu, kuma ba wanda zai shaide shi da tsoma baki a lamuran kotu.
Duk da haka shugaban ya ce zai duba bukatar tsohon.
A na tuhumar Kanu da laifin cin amanar kasa da ta’addanci a shari’ar da za a cigaba da yi ma sa a ranar 19 ga watan Janairu 2022.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.