• Wed. Jun 29th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

A BA DA DAMA JAMA’A SU MALLAKI BINDIGA DON KARE KAN SU-SHEIKH ZAKARIYYA

Shehun malamin Islama da ke tafsiri a Abuja Hussaini Zakariyya ya bukaci gwamnatin Najeriya ta ba wa mutane damar mallakar bindiga don kare kan su yayin da tsaro ke kara tabarbarewa.

Sheikh Zakariyya ya baiyana bukatar a taron rufe majalisar tafsirin sa na bana hijra 1442 a masallacin jumma’a na Othman bin Affan da ke Wuse 2 a Abuja.

Malamin ya ce mutane ba za su zura ido wasu miyagu su far mu su ba tare da tabuka wani abu na kare kai ba ko da kuwa ta hanyar mallakar wani makami ne mai rejista.

Hakan, a nazarin malamin zai sa miyagun irin su san cewa ba su kadai ne ke da hurumin rike makamai ba, don za su iya kwasar kashin su a hannu in su ka tinkari jama’ar da ke kwana cikin shirin ko-ta-kwana.

Da a ka ja hankalin malamin kan fargabar in mutane su ka mallaki makamai za su iya amfani da su wajen son zuciyar fitinar bangaranci da kabilanci ko ma addini, malamin ya ce duk wanda a ka yi wa rejista dole ya bi ka’idar amfani da makamin sa wajen kare kai ba wai shiga wata fitina ko takalar fada ba.

Sheikh Zakariyya ya nuna takaicin tamkar gwamnati a Najeriya ta gaza ko ta yi kasa a guiwa wajen kare rayukan mutane, don haka ya dace mutanen su tashi tsaye wajen kare kan su daga duk wani farmaki.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “A BA DA DAMA JAMA’A SU MALLAKI BINDIGA DON KARE KAN SU-SHEIKH ZAKARIYYA”
  1. Its like you read my mind! You appear to know a lot about this, like you wrote the book in it or something.
    I think that you could do with a few pics to drive the
    message home a little bit, but instead of that, this
    is wonderful blog. A fantastic read. I’ll definitely be back.

Leave a Reply

Your email address will not be published.