_TPL.USMAN NADADA RUWA NE MAI AIKI SANNU A SIYASANCE….._

Alkalamin Yakubu Lawal

Tpl. USMAN NADADA NGs,Toprec,Nitp,Rtp, NATE. Wanda yakasance kwararren Mai tsara birane(TOWN PLANNER) a ilmance, dan siyasa ne da rawar da yake takawa da karbuwarsa ga jama’a kawai za ta iya yi masa gurbi a siyasance,domin ba a kira sa tsohon dan siyasa ba,saboda a shekaru har yanzu bai yi shekarun ajiye aikin gwamnati ba, duk da cewar ya fara aikinsa na gwamnati da digiri na biyu a matsayin matsakaicin ma’aikaci inda har ya kai matsayin shugaban Hukumar da ya yi aiki a cikinta,wato Hukumar Tsara Birane ta Jaha.

Hon.Usman Nadada dan siyasa ne daga tushe da ya dauki lokaci ya na taka rawa a siyasa tun daga tushiya har zuwa sama,domin siyasarsa ta yi shura tun daga Mazabarsa ta Wakilin Kudu(II) ta Karamar Hukumar Katsina, a Karamar Hukumar dama Jahar Katsina baki daya,inda yakan taka rawar shugaban masu ruwa da tsaki ko waninsa

Wannan shuwura da Alhaji Usman Nadada ya yi ta sanya shekaru dadama a mafi yawancin tarukan siyasa ‘yan bangar siyasa da Sojojin Baka sukan cigaba yi masa irin shaguben da yan siyasa ke so , saboda yana da hannun baiwa(KYAUTA)amman wannan zance bai bata kwadaita ma shi wani abu a zuciya ba,sai dai yakan ce “Ka yi man fatan abinda ke alhairi ya fi ka ce Allah ya yi mani kaza” sannan sau da yawa yakan taka birki ga Sojojin Bakan dake zuwa gidajen Rediyo don siyasantar dashi, _duk don shi ruwa ne mai aiki sannu_ . Duk da cewar,a gidin maganin siysar Katsina yake,wato inda siyasar take daukar Harami kuma take Makati

Duk da matakan da yake dauka na ganin mutane sun masa fatan alkhairi kawai, a maimakon hada addu’ar da wani mukami.

Wannan fata ta cigaba da ruruwa musamman daga shekarar 2019,a lokacin da aka baiwa Hon.Usman Nadadan Kwashinan Ma’aikatar Kasa da Sufiyo, inda har ‘yan Jarida da yake da alaka mai kyawo dasu, sukan tuntubesa da irin wannan zance na makomar siyasarsa, inda amsarsa takan zama goce-goce,sannan jaridu dadama da masu fashin baki a kan makomar siyasar Katsina sukan lisafto da sunansa, musamman idan aka zo fagen neman mafita ta wanene zai gaji Kujerar Gwamna a Jahar Katsina, duk wannan bai sanya Hon.Usman Nadada yasa yace komai ba kai tsaye, a kan sharhi da fashin bakin da ake a kan matsayin da ake alakantashi da shi ,duk da cewa a gaba-gaba yake a gidan siyasar da duk wadanda suke fitowa a siyasance tun daga dawowar dimokaradiyya a 1999,a Jahar Katsina sukanyi shura ne idan aka alakanta siyasarsu da gidan wannan hamshakin mai kudin a Jahar Katsina(Alhaji Dahiru Bara’u Mangal).

Anan nima ina shedar cewar, Hon. Usman Nadada horon siyasar gidan Dahiru Mangal ne, kuma yasha nonon da bai zubar ba, don saboda bukatarsu al’umma su amfana ga siyasa,basu ba kai tsaye,tunda har gobe baka taba ganin dansu ko waninsu da suke nema wa gurbin siyasa

Tunda ake masa irin wadannan tambayoyi sau daya naga Hon. Nadada ya bayarda amsa a wata Jarida ta Kasa da Kasa ta turanci Mai Suna’Housing Circuit Magazine’ da suka yi masa tambaya kai tsaye cewar; Idan aka tsayar da kai takarar Gwamna a Jahar Katsina za ka yi ko ko?. Anan ne ya kada baki yace”I _WILL ACCEPT IF _NOMINATED. IF IAM NOT NOMINATED I WILL NOT GO AND HARASS MYSELF INTO LOOKING FOR THE GOVERNORSHIP. IAM NOT SCARED OF DEPEAT BECOUSE ONCE U ARE A MAN U HV TO STAND ON UR FEET; IT IS MY POLICY TO GET WHAT I CAN TO ASSIST MY PEOPLE. IT IS NOT NECESSARILY THAT U HV TO CONTEST FOR U TO ASSIST OR HELP UR PEOPLE. IAM NOT UNDER PRESSURE TO CONTEST OR SOMETHING LIKE”.Pg.25(5/May/2021)._
Wannan ya nuna Hon. Usman Nadada Ruwa ne da yake tafiya a hankali, kuma da sannu cikin ikon Allah zai yi nisan da zai cika kogunan da ke kusa da nesa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *