Zargin Badakalar Biliyan 80: Buhari Ya Dakatar Da Babban Akawun Kudi Na Najeriya

Ministar ma’aikatar kudi ta Najeriya Hajiya Zainab Ahmad ta sanar da dakatar da babban akawuntan kudi na kasa Alhaji Ahmad Idris daga mukamin sa

sanarwar mai dauke da sa hannun ministar ta bayyana cewa dakatarwar ta biyo bayan binciken da hukumar EFCC ke yi masa bayan da ta kama shi

Kamar yadda ta bayyana, dakatarwar na da nufin baiwa hukumar cikakkiyar damar binciken dakataccen babban akawun akan zargin da ake masa na satar kudin kasa kimanin Naira bilyan tamanin(#80 billion)

Sanarwar ta umarci babban akawun da ya kauracema wajen aikin sa tare da kauce ma hudda da dukkanin ma’aikatan ofishin har sai dai idan gayyatar shi akayi domin bayyana a gaban kwamitin bincike

An kuma umarce shi da ya shirya amsa goron gayyata akoda yaushe domin amsa tambayoyi da za’a iya kiran shi domin ya bada ba’asi akan badakalar kudin da ake zargin sa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *