An gudanar da jana’izar mutum 15 da suka rasu a sakamakon hatsarin jirgin ruwa wato kwale-kwale a jihar Katsina.
Kwamanshinan Ma’aikatar kula da Ayyukan Ƙananan Hukumomi da Masarautu na Jihar Katsina, Hon Ya’u Umar Gwajo-Gwajo ya halarci jana’izar mutum goma sha biyar da suka rasu a sakamakon hatsarin jirgin ruwa wato kwale-kwale a madatsar ruwa ta Sabke dake Ƙaramar Hukumar Mai’adua.
Rahotanni sun ce hatsarin ya faru ne a jiya Laraba da dare a inda wani jirgin ruwa ɗauke da mutane da dama ya kife wanda hakan ya yi sanadiyar hasarar rayuka 15.
Tuni dai aka gudanar da jana’izar mamatan yau Alhamis da misalin ƙarfe 7:30 na safe a garin Tsabu dake Ƙaramar Hukumar Mai’adua.
Hon Gwajo-Gwajo wanda ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka samu halartar jana’izar ya bayar da tallafin naira dubu dari da hamsin tare da buhun masara shida nan take domin bayar da sadaƙa ga iyalan mamatan.