Kotu ta yankewa wani mutum mai shekaru 25 hukuncin daurin rai da rai a Jigawa

Babbar Kotun Jihar Jigawa da ke Birnin Kudu ta yanke wa wani matashi dan shekara 25 hukuncin daurin rai da rai bisa samunsa da laifin fyade.

Da yake yanke hukuncin a ranar Alhamis, Mai shari’a Musa Ubale, ya ce kotun ta samu Musa Mu’azu dan unguwar Zango da ke Birnin Kudu da laifin yi wa wata yarinya ‘yar shekara 14 fyade, wanda ya saba wa sashe na 282 (1) na kundin dokokin. .

Kotun ta kuma yankewa wani mai suna Haruna Ali hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari bisa samunsa da laifin yi wa wata yarinya fyade a kauyen Yarma da ke karamar hukumar Birnin Kudu a jihar Jigawa.

Hausa Abcnews ta rawaito cewa, Mai shari’a Musa Ubale ya kuma yanke hukuncin daurin shekaru 10 a gidan kaso kan wani mai laifi Ahmed Isa, mazaunin garin Jama’are na jihar Bauchi bisa samunsa da laifin fashi da makami wanda ya saba wa sashe na 298 na kundin dokokin hukumar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *