Daga Abdullahi Alhassan Kaduna.
Wani mai rake da Sarautar Gargajiya wato Banagan Tudun Wadan Kaduna, kuma Shugaban Tsangayar kimiyar Sinadarai,wato Applied Science,a Turance,Dr,Nuhu Abdullahi, yace horar da Marayu Sana’o’i da kuma tallafa musu kan ilmi zai magance matsalolin da suke ciki.
Dr, Nuhu Abdullahi,ya baiyana haka ne, a yayin taron raba kayan a bincin Sallah ga Marayu wanda Gidauniyar Tallafawa Marayu na Abakwa dake karamar hukumar Kaduna ta arewa ta gabatar.
Inda ya kara da cewar,laile hakki ne na jama’a da suriga tallafawa Marayu kasancewar su,Yayan mu ne, kuma Allah ya dora mana nauyin kula da sha’anin su, don muma nuna lya Mutuwa mu bar Marayun kuma Allah zai kawo masu yi mana.
Dr, Abdullahi, wanda shine shugaban taron ya jaddada cewar ba kawai basu abinci ba da Sallah ko azumi ba ,A’a ya zama ana sasu Makarantu dama daukar nauyin su,tare kuma da koyar dasu Sana’o’in daban -daban don dogaro dakai anan gaba.
Shi kuwa a nashi Jawabin yayin taron shugaban kungiyar tallafawa Marayun dake Abakwa a karamar hukumar Kaduna ta Arewa, Mallam Abubakar lmam,cewa yayi wan nan bashi ne karo na farko ba da suke tallafawa Marayu ba, kuma a wan nan abune da muke yi duk shekara ayau mun tallafawa Marayu da Marasa karfi kamar 900.
lnda muka raba kayan Sawa na Sallah,wato Sutura kenan,sai kuma abin cin Sallah ga lyayen Marayu dama marasa Karfi don dafawa ya yansu da Sallah.
A wan nan kungiyar muna tallafawa Marayun da koyar da su Sana’o’in da zasu dogara da kan su, a nan gaba kaga kenan nan da lokaci kadan zai dai suma su tallafawa wasu.
Mallamin addinin, yayi kira ga masu hannu da shuni kan tallafawa Marayu, Mata ,dama karasa karfi cikin al’umma don ganin an tallafawa masu da abubuwan da zasu yi amfani da shi musamman ma lokacin bukata sosai.