Gomnatin Zamfara ta Gwangwaje Yan Jarida da Tiyar Shinkafa 4 su Raba

Gwamnatin jihar Zamfara ta Baiwa Yan Jarida wakilan kafafen yada labarai na kasar nan a Gusau Kyautar Tiya Hudu ta Shinkafa da Tiya Daya ta Suga albarkacin watan Ramadan.

Jaridar ‘Smarts News’ ta kalato labarin cewa, kungiyar ‘yan jarida masu aikewa da Rahitanni su 25 ne Kuma an Basu Tallafin domin su ji dadin azumin watan Ramadan na shekarar 2022.

Kunshin wanda ya fito ta hannun shugabancin kungiyar ta NUJ ta jihar Zamfara, wanda daraktan kula da harkokin gwamnati, Alhaji Aliyu Sani Wanda aka fi sani da BK ya mika wa kungiyar, ya ce adadin kayan azumin da aka bayar na sama da Yan Jarida na Kungiyar NUJ 200 a jihar, sun kunshi Buhunan Shinkafa Biyar da Buhu Biyu na Sukari.

A cewar BK, gwamnatin jihar ta yi la’akari da wasu matsaloli da aka fuskanta a lokacin azumin watan Ramadan hakan yasa Gomnati tayi a’akari da yawan rassan Kungiyar guda Tara (9) da yawan ‘yan jarida da ke aiki a cikin jihar ta bada Tallafin ta hannun majalisar NUJ a jihar don a raba kamar yadda ya kamata. zuwa adadin membobin da aka lissafa.

Da suke karbar kayayyakin, shugaban kungiyar NUJ na jihar Zamfara, Kwamared Bello Ibrahim Boko da shugaban kungiyar masu aiko da rahotanni, Kwamared Sani Haruna Dutsinma, sun godewa Gwamna Bello Mohammed Matawalle da wannan karimcin, inda suka tabbatar da cewa zasu tabbatar kowane mamba na Kungiyar ya samu nashi kaso.

To saidai akasarin Mambobin suna ta ribidin Lebo da Cece kuce akan kayan, Wanda wasu ke ganin rashin kimanta Aikin Yan Jaridar ne wasu Kuma ke nuna baya In gomnatochin da suka gabata ke Baiwa Kungiyar Dinbin Buhuwa domin rabawa a tsakanin su.

Wani Mai sharhi akan al’amuran yau da kullum a Nigeria Dan Jarida Mai Aiki a Birnin Tarayya Abuja, wato Al-Amin Usman Bappa ya bayyana takaici akan lamarin, Wanda yace “Duk da yake ba dole ba ne Kuma kyauta ce, Amma ya dace a mutunta Mai mutunchi”

“Ai ba Haushe yace ko ba kayi kana yiwa Wanda ke Yi Maka” yayi Karin bayani.

Binciken da ‘Smarts News’ yayi ya Gano cewa, daukacin Yan Jaridar masu aikewa da labarai daga Zamfara su Ashirin da Biyar Dukanin su magidan ta ne, masu iyali.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *