‘
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Osun ta kama wani mafarauci, wanda ake zargin ya harbe har lahira, limamin kauyen Alaguntan mai shekaru 78 da haihuwa, a Orile-Owu, cikin karamar hukumar Aiyedaade.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Yemisi Opalola, ne ta bayyana haka a yayin baje kolin wadanda ake zargi da aikata laifuka a hedikwatar ‘yan sandan jihar da ke Osogbo ranar Talata. Ta ce: “A ranar 17 ga Afrilu da misalin karfe 11:30 na safe, wani mai korafi daga yankin Ogbere Oloba da ke Ibadan ya kai rahoto a ofishin ‘yan sanda cewa, an harbe mahaifinsa Adegun Yusuf mai shekaru 78, Limamin kauyen Alaguntan da ke Orile-Owu.
“Daga baya an kama wanda ake zargin kuma ya amsa laifin da ake zarginsa da shi.”
Wanda ake zargin ya bayyana cewa, “yana tafiya farauta ne sai ya ga wata barewa a daji, sai ya harbe ta da bindigarsa, amma ya yi mamaki lokacin da ya je ya dauko ta, sai ya taras da Baba Imam kasa.” Opalola ta ce, za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu bayan an kammala bincike. Hakazalika, kakakin ‘yan sandan ta ce rundunar ta kuma kama wani matashi dan shekara 27, wanda ake zargi da aika sakwanni ta wayar tarho ga wani dan majalisa a Osun da wani alkali, yana barazanar sace su da ‘ya’yansu. Kakakin ‘yan sandan ta ce, wanda ake zargin ya aike da sakonnin barazana ga mutanen, inda ya bukaci a biya su N500,000 zuwa Naira miliyan 2, idan ba sa son a yi garkuwa da su tare da ‘ya’yansu.
Ta ce, a lokacin da aka kai rahoton lamarin, jami’an tsaro na ‘yan sanda sun dauki mataki, inda ta kara da cewa, bisa namijin kokarin da aka yi, an gano lambar wayar da aka yi amfani da ita wajen aikewa da sakon barazanar, inda aka kama wanda ake zargin. Opalola ta ce, sauran wadanda ake zargin da rundunar ta kama, sun hada da wasu maza uku daga Ile-Ogbo, wadanda ake zargin sun kashe wata mata ‘yar shekara 53, suka yanke kai da hannu da kafafuwa tare da cire mata zuciya saboda samun kudi. Ta ce an kuma kama wasu mutane uku da ake zargin ‘yan fashi da makami ne, wadanda suka saba bi wajen hada-hadar POS daga shagunansu zuwa gidajensu da ke Ikirun, sannan kuma suka yi musu fashi da kudi da kuma dukiyoyinsu. Opalola ya kara da cewa, an kama wani da ake zargin dan fashi da makami ne a unguwar Aregbe da ke Osogbo da jami’an ‘yan sanda suka kama a lokacin da yake kokarin kwace wani babur din haya da fasinjansa da wayoyinsu.
Ta ce za a gurfanar da dukkan wadanda ake zargin a gaban kotu bayan an kammala bincike. Kakakin ‘yan sandan ta yi kira ga mazauna yankin da su agaza ma ‘yan sanda ta hanyar samar da bayanan da ake bukata a kan lokaci domin kawar da miyagun laifuffuka da aikata laifuka a jihar.