Dattawa a jihar Ekiti sun yi gargadi game da tashin hankali a lokacin zabe

Dattawa masu kishin kasa a  jihar Ekiti da ke aiki a karkashin kwamitin dattawan Ekiti, sun yi gargadi kan tashe-tashen hankula da sayen kuri’u a zaben gwamna da za a yi ranar 18 ga watan Yuni a jihar.
Dattawan yankin sun kuma bukaci al’ummar jihar da su gudanar da rayuwarsu cikin lumana kafin zabe da lokacin zabe da kuma bayan zaben.
Sun yi wannan magana ne a Ado Ekiti babban birnin jihar, yayin wani taron karawa juna sani na kiwon lafiya da aka shirya wa mambobin kungiyar a jihar.
Kwararru a fannin kiwon lafiya da abinci mai gina jiki, sun baiwa dattawan wasu shawarwari kan yadda za su yi rayuwa cikin koshin lafiya a lokacin da suka tsufa.
Da yake jawabi a madadin kungiyar, Sir Lawrence Egunjobi ya ce kungiyar da ke aikin ci gaban jihar ba ta siyasa ba ce. Egunjobi wanda ya bayyana zabuka na lokaci-lokaci a matsayin alamar dimokuradiyya ya ce, “Ya kamata zaben ya kasance na dimokuradiyya, amm lokacin da aka hada da sayen kuri’u, ba dimokuradiyya ba ce sai dai kudi”.
Da yake addu’ar Allah ya sa a gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali ba tare da tashin hankali ba, ya ce kwamitin za ya goyi bayan duk wanda ya ci zabe domin tabbatar ci gaban jihar. A cewarsa, “Don haka muna kira ga iyaye da su ja kunnen ‘ya’yansu da kada su bari a yi amfani da su a matsayin ‘yan daba.” Kada ‘yan siyasa su shiga tashin hankali.” “Dole ne ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro su kasance masu adalci ga kowa da kowa, kuma su gudanar da ayyukansu ba tare da tsoro ba.” Sai ya yi kira ga masu zabe da su fito ranar zabe su zabi dan takara, su hada kai da duk wanda ya ci zabe domin ciyar da jihar gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *