Gwamnatin tarayya na shirin samar da Ayyuka milyan 21 ta hanyar Zuba Jari

Gwamnatin Tarayya na shirin samar da ayyukan yi milyan 21, ta hanyar zuba jari mai yawa a kan ababen more rayuwa a cikin shekaru uku masu zuwa.
Karamin Ministan Kasafin Kudi da Tsare-Tsare na Najeriya Clem Agba ne ya bayyana hakan jiya a Abuja, a wajen wani taron karawa juna sani na tsawon kwanaki biyar akan ‘ Tsarin Sa Ido da daidaiton Tattalin Arzikin Kasa don Aiwatar da Shirye-shiryen Kasa Na Biyu’. 
Ya ce shawarar samar da ayyukan yi miliyan 21 na daya daga cikin sakamakon shirin raya kasa na shekarar 2021-2025, wanda shirin ke kokarin fitar da mutane milyan 35 daga kangin talauci nan da shekarar 2025.
Ya ce hakan ne zai sa a cimma burin gwamnati mai ci na fitar da ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga kangin talauci nan da shekarar 2032.
Ya kara da cewa shirin na ci gaban, zai kuma tabbatar da cewa Najeriya ta nuna karfinta a dukkan bangarorin tattalin arziki.
Agba ya ce, ma’aikatar sa na shirin kammala ci gaban ajandar Nijeriya ta 2050, wanda shi ne tsarin ci gaban kasa don maye gurbin kudurin kasa na  20:2020.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *