Jam’iyyar APC ta fitar da cikakken jadawalin gudanar da zabe


Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta fitar da jadawalin ayyuka da jadawalin gudanar da zabukan shekarar 2023 mai zuwa.
Jam’iyyar ta ce an yi hakan ne bisa tanadin dokar zabe ta shekarar 2022 kamar yadda aka yi mata kwaskwarima da kuma jadawalin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC. Idan za a tuna cewa, kwamirin Zartarwa na kasa na  jam’iyyar APC ya yi taro, tare da mika iko ga kwamitin ayyuka na kasa na jam’iyyar. Bayan wannan ci gaba ne kwamitin zabe na APC, ya kayyade Naira miliyan 100 na fom domin tsayawa takarar shugabancin kasa da kuma fayyace fam din takarar gwamna da ya kai Naira miliyan 50, sai Majalisar Dattawa Naira miliyan 20, sai kuma Majalisar wakilai Naira miliyan 10, da kuma na majalisar jiha akan Naira miliyan biyu.
To sai dai kuma duk da korafin da jama’a da daidaikun kungiyoyi da kuma ‘yan takara ke yi, jam’iyyar mai mulki ta tsaya tsayin daka kan wannan farashi nata, inda a yanzu ta ke sa ran ganin zaben fidda gwani da sauran ayyukan da za ta yi kafin zabe. 
Haka kuma jam’iyyar ta saki asusu guda bakwai daga bankunan Najeriya daban-daban inda ya kamata masu bukata su fara yin ajiya. Nakasassu da mata da matasa masu shekaru 40 zuwa kasa, ba a sa ran su biya kudin fam din takara gaba daya. Haka kima, Mata da nakasassu za su sayi fom ɗin Nuna sha’awa ne kawai, yayin da za su sami fom ɗin tsayawa takara kyauta. Yayin da su kuma matasan za su biya rabin kudin fom na tsayawa takara tare da bayar da cikakken biyan kudin nuna sha’awar karbar fam.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *