Gawawwaki dari da tara aka gano bayan gobarar mai a jihar Imo

Akalla mutane dari da tara ne suka kone kurmus bayan da wata gobara ta kama wata haramtacciyar matatar mai da ke Abacheke Kpofire a yankin Egbema a karamar hukumar Ohaji/Egbema ta jihar Imo.
Kafar yada labarai ta DAILY POST ta tattaro cewa, lamarin da ya faru a daren Juma’a ya yi sanadiyyar  rasa rayuka da dama, yayin da wasu suka samu munanan raunuka.
Shugaban ayyuka na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa, Mista Ifeanyi Nnaji, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda  ya kara da cewa, mutane 20 ne kawai suka mutu a gobarar.
Sai dai a wani karin haske a  jiya Asabar, Nnaji ya ce ya zuwa yanzu an gano gawarwakin mutane 109, yayin da wasu kuma suka bace bat. Ya ce, “Abin ya yi muni fiye da yadda muka yi hasashe. Ya zuwa yammacin yau, mun kirga gawarwaki 109 a kasa, yayin da wasu da dama suka fada cikin kogin wasu kuma sun mutu a cikin matatar man.”
Kwamishinan albarkatun man fetur na jihar Imo, Goodluck Opiah, ya bayyana cewa, mai gudanar da haramtacciyar matatar man mai suna Okenze Onyenwoke, a halin yanzu yana hannun sa.
An kuma bayyana cewa, kimanin motoci shida ne suka kone yayin la

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *