–
Babban daraktan hukumar masu yi ma kasa hidima na kasa (NYSC), Manjo-Janar Shuaibu Ibrahim, ya ce kare muhalli da tsaftar muhalli ba za a iya raba su ba don samar da kwanciyar hankali, lafiya da cigaban muhallin.
Janar Shuaibu ya bayyana haka ne a jiya Asabar a Bauchi a lokacin da yake kaddamar da shirin tsaftace muhalli na hukumar masu hi ma kasa hidima na kasa a jihar Bauchi.
Janar Shuaibu wanda ya samu wakilcin kodinetan hukumar na jihar Bauchi Namadi Abubakar, ya sanar da ‘yan kungiyar cewa, aikin tsaftar muhalli mai taken “ tsaftataccen muhalli shi ne mai amfani ga inhatacciyat lagiya da tsawon rai” yana gudana ne a dukkan jihohin kasar nan 36 da babban birnin tarayya Abuja. Shugaban ya ce, tsaftace muhalli lamari ne da ya shafi duniya baki daya, shi ne muhimmin abin da ake bukata na rigakafin cututtuka, inda ya kara da cewa dole ne a hada kai da kowane dan kasa domin shiga cikin samar da tsaftataccen muhalli.
A cewarsa, “Kamar yadda kuka riga kuka sani, an amince da tsaftar muhalli a duk duniya a matsayin daya daga cikin muhimman abubuwan da ake bukata na rigakafin cututtuka da kuma karuwarsu, zuwa yawan annoba. A kan wannan batu, dole ne a kara kaimi wajen fadakar da jama’a musamman mazauna karkara game da illolin da ke tattare da rashin tsafta musamman kan hana gurbacewar abinci da ruwa da muhalli baki daya.”