A yau Assabar aka binne Oba Adeyemi III a tsohon garin Oyo.
Adeyemi ya rasu ne a ranar Juma’a, a asibitin koyarwa ta jami’ar Afe Babalola dake Ado Ekiti.
Tuni dai aka kai gawar Alaafin na Oyo din a fadar sa.
Tun da farko, shugaban kungiyar Oyomesi,Yusuf Ayoola ya bayyana cewa, za a yi jana’izar marigayi Alaafin a yau.
Ya ce an yi dukkan abubuwan da suka dace.