Hambararren  shugaban kasar Guinea Alpha Conde ya sami ‘yanci

Gwamnatinn mulkin soja ta kasar Guinea ta sako tsohon shugsbs Alpha Conde.

Hambararren shugaban Alpha Conde a halin yanzu yana da ‘yanci, kuma yana iya karbar baki, in ji gwamnatin mulkin sojan da ta hambarar da shi.

Conde ya zama zababben shugaban kasar Guinea na farko ta hanyar dimokuradiyya a shekarar 2010, amma jami’an soji sun hambarar da shugaban mai shekaru 84 a shekarar da ta gabata,inda aka maye gurbinsa da Kanar Mamady Doumbouya.

An ba shi damar zuwa kasar Hadaddiyar Daular Larabawa don jinya a watan Janairu, inda ya dawo Guinea a ranar 10 ga Afrilu.

Jam’iyyarsa ta Rally of the Guinean People (RPG) ta ce, da gaske bai samu ‘yanci ba kafin ko bayan tafiyar tasa, kuma ta bukaci ‘yancinsa na gaba daya ba tare da wani sharadi ba.

Domin tabbatar da kiran nata, jam’iyar ta RPG ta dakatar da halartar taron sulhu na kasa da gwamnatin mulkin soja ta shirya domin nuna adawa da tsare shi.

A wata sanarwa da gwamnatin mulkin sojan kasar ta fitar da yammacin jiya Juma’a ta ce, shugaba Doumbouya yana sanar da kasa da duniya baki daya cewa, a karshe tsohon shugaban kasar ya samu ‘yanci.

Sanarwar ta ce,”Yayin da hambararren shugaban yake ci gaba da cin gajiyar isasshiyar kariya, zai iya karbar tawagar danginsa da ‘yan siyasa da abokai na kusa,”.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Conde zai ci gaba da zama a gidan matarsa ​​da ke Conakry babban birnin kasar har sai an gina nasa gidan a unguwar Kipe.”

“Mutunci da haɗin kai na farfesa Alpha Conde za su kasance abin kiyayewa a koyaushe,” in ji sanarwar.

Juyin mulkin sojin ya biyo bayan zanga-zangar da aka yi kan nasarar da Conde ya samu na neman wa’adi na uku a kan karagar mulki, wanda masu suka suka ce ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar.

Shugaba Doumbouya, wanda aka rantsar a matsayin shugaban rikon kwarya, ya yi alkawarin maido da mulkin farar hula, amma ya ki amincewa da matsin lambar da kasashen duniya suka yi masa na ayyana rana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *