Kakakin gwamnatin kasar Iran Ali Bahadori Jahromi ya yi karin haske kan matsayar Iran kan lamarin masallacin Qudus, yana mai cewa daidaita alaka tsakanin wasu kasashen musulmi na Larabawa da Kasar Isra’ila ya karfafa danniyar kasar ga Palastinawa.
Da yake jawabi ga taron manema labarai a yau Talata, Bahadori Jahromi ya yi tsokaci kan tuntubar da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta yi da kungiyar Hamas, da tuntubar ministocin harkokin wajen wasu kasashen musulmi. Har ila yau ya yi nuni da wata wasika daga Iran zuwa ga babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC dangane da yin Allah wadai da ayyukan gwamnatin kasar ta Isra’ila.
A halin da ake ciki kuma tun da farko kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Saeed Khatibzadeh, ya bayyana cewa dole ne musulmi su tashi tsaye wajen goyon bayan al’ummar Palastinu. Sakamakon ci gaba da tashin hankali da wuce gona da iri da gwamnatin Isra’il ke yi. Tun bayan shiga watan Ramadan, da dama daga cikin Palastinawa ne suka rasa rayukansu, tare da jikkata daruruwa.
A wani bangare na jawabin nasa, Bahadori Jahromi ya yi tsokaci kan karar da aka kai tsakanin kamfanin iskar gas na Iran da wani kamfanin kasar Faransa, inda ya ce kamfanin na Faransa ya yi ikirarin dala miliyan 27 da kuma ikirarin da kamfanin na Iran ya yi na dala miliyan 13. Ya kara da cewa a karshe kotun ta kada kuri’ar amincewa da Iran kuma za a biya dala miliyan 1.5 ga Iran.