An jefa iyalan wani dan kasuwa mai suna Yahaya Hassan Musa mai shekaru 39 cikin alhini yayin da aka tsinci gawarsa a cikin daji sa’o’i kadan bayan da wadanda suka sace shi suka karbi kudin fansa Naira milyan shida.
Lamarin dai ya fara ne a ranar Alhamis din da ta gabata, a lokacin da mamacin, mai aure da ’ya’ya biyu, yana dawowa daga Cotonou Jamhuriyar Benin, bayan wata tafiya ta kasuwanci, inda aka yi garkuwa da shi a wani dajin da ke unguwar Mopa a jihar Kogi, inda masu garkuwa da mutanen suka bukaci Naira milyan 10, yayin da daga baya aka kai milyan shida.
Da yake bayyana lamarin, dan uwan marigayi Yahaya, Abubakar Hassan Musa, wanda ya kai Naira milyan 6 ga masu garkuwa da mutane ya ce, dan uwansa ya kan ui tafiya ta sama a duk lokacin da zai yi tafiya, amma a wannan balaguron ya yanke shawarar komawa ta kasa.
Ya ce, “Masu garkuwa da mutanen sun bukaci in kai kudin wani dajin Kabba. Na je na kai kudin. Sai suka nusar da ni wurin da zan sadu da shi, amma ban same shi ba. Na kwana a cikin dajin ni kadai. “Washegari na ci gaba da bincike har sai da wata mata da aka yi garkuwa da ita tare da dan uwana ta kira ni ta ce sun kashe shi kafin ma karbar kudin fansa, amma ba ta san inda suka jefar da gawarsa ba. “Na koma garin da ke kusa na yi hayar mafarauta domin su koma cikin daji su nemo gawar. Bayan mun yi tafiyar kilomita da yawa, sai muka iske gawarsa tana rubewa.” Ya ce saboda ba su samu motar da za ta dauki gawar ba saboda rubewar da ta yi, sai suka binne shi a daji kamar yadda addinin Musulunci ya tanada bayan tuntubar iyalansa a Kano