Yan bindiga sun kashe mutane hudu a Kaduna

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari tare da kashe mutum hudu da yin garkuwa da wasu mazauna unguwar Bulus da ke karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna a daren jiya Lahadi.
Wani mazaunin yankin, Mista Yohanna Magaji, ya shaida wa DAILY POST a Kaduna, a yau Litinin  cewa, ‘yan bindigar da yawansu ya haura 100 ne suka far wa al’ummar a daren ranar Lahadi, inda suka fara harbe-harbe ba da jimawa ba, a daidai lokacin da mazauna unguwar da suke cikin barci suka farka suka fara gudu. “’Yan bindigar sun zo ne da misalin karfe 11:00 na daren Lahadi, kuma suka fara harbe-harbe kai tsaye. Mutanen kauyen da suke cikin barci mai nauyi, kwatsam suka farka, da jin karar harbe-harbe. Suka fara gudu, duk a ruɗe suke. An kashe mutane hudu,” in ji shi.
A cewarsa, an kai wadanda suka mutun zuwa dakin ajiye gawa na asibiti. Ya yi kira ga jami’an tsaro da su taimaka wajen tabbatar da tsaron al’umma, domin ‘yan fashin sun farmaki al’ummar a karo na hudu tun daga watan jiya.
Har zuwa hada wannan rahoto ba ji ta bakin  kakakin ‘yansanda na jihar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *